IQNA

Nasr Al-Shommari: Ta Hanyar Tunanin Marigayi Imam Khomenei Amurka Da Isra’ila Za Su Sha Kasa

22:55 - February 11, 2021
Lambar Labari: 3485640
Tehran (IQNA) kakakin kungiyar gwagwarmaya ta Nujba daya daga cikin rassan Hashd Al-shaabi a Iraki ya bayyana cewa, ta hanyar mahangar gwagwarmayar Imam Khomeini ne Amurka da Isra’ila za su kasa.

A cikin zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna, Injiniya Nasr Al-Shommari kakakin kungiyar gwagwarmaya ta Nujba daya daga cikin rassan Hashd Al-shaabi a Iraki ya bayyana cewa, ta hanyar mahangar gwagwarmayar Imam Khomeini ne Amurka da Isra’ila za su kasa a cikin wannan zamani.

Ya ce idan aka yi la’akari da yanyin duniyar yau, akwai abubuwa da dama da suke bukatar sauyi na hakika, wanda kuma hakan ba za ta samu ba sai ta hanyar kawo karshen mamayar Amurka da Isra’ila a kan harkokin siyasar duniya da tattalin arzkinta da batun na tsaro.

Abin da za a gani shi ne Amurka da turawan yamma sun su ne suke iko da duniya saboda sun mamaye wadannan bangarori a matsayi na kasa, ta yadda sauran kasashen sun zama ‘yan kallo ko kuma sun zama tamkar bayi ga Amurka da kasashen turai.

Ida nana son duniya ta zauna lafiya, sai an kawo karshen mamayar da turawa suke yi wa duniya a siyasance da kuma ta fuskar tattalin arziki da soji, sannan ne kasashen duniya za su zama masu ‘yanci, idan kuma bah aka ba, to al’ummomin duniya za su ci gaba da zama bayin turawa.

Mahangar marigayi Imam Khomeini ita ce al’ummomin duniya su zama masu ‘yanci a cikin dukkanin harkokinsu, tare da daina dogaro da turawa, su dogara da kansu, wanda hakan ne zai ba su damar karya karfin Amurka na siyasa da tatatlin arzikinta da kuma mamaye duniya da ta yia dukkanin bangarori.

Kuma wannan shi en abin da marigayi Imam Khomeini ya yi a aikace ta hanyar juyin juya halin da ya jagoranta a Iran, da kuma yadda ya mayar da kasar Iran ami 'yanci, maimakon yadda ta kasance a  baya a matsayin baiwa 'yar kore ga Amurka da yahudawa, kamar yadda a halin yanzu manyan kasashen musulmi suke a wannan matsayin, inda suka zama su ne masu aiwatar ad siyasar Amurka da yahudawa a kan kasashen msuulmi.

3953121

 

captcha