Shugabar jam’iyya mai mulki ta kasar kuma tsohuwar shugaba Aung San Suu Kyi, ta shiga hannun sojojin da suka yi juyin mulki bayan da suka bayyana cewa jam’iyya mai mulki ta National League for Democracy ta tafka magudi a zaben ‘yan majalisar da aka gudanara watan Nuwamban da ya gabata.
A zaben dai jam’iyyar ta National League for Democracy ta samu gagarumin rinjaye, wanda ya bata damar ci gaba da gudanar da mulki, duk kuwa da cewa alokacin sojin sun nuna damuwa kan abubuwan da suka yi zargi na tafka magudi.
Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Janar Min Aung Hlaing zai ci gaba da rike iko da kasar har zuwa nan da shekara guda mai zuwa.
Sojojin na Myanmar sun sanar da manyan sauye-sauye a majalisar gudanarwar kasar, wata sanarwa da sojojin suka fitar, ta bayyana cewa, karkashin sabon garanbawul din da suka yiwa majalisar zartarwar kasar, an nada sabbin ministoci sha daya da za su kula da ma’aikatun kasar, yayin da aka tube mataimakan ministoci ashirin da hudu daga mukamansu.
Sai dai kuma, ba a sauya babban alkali da alkalan kotun kolin kasar ba, wannan mataki na zuwa ne, bayan da ofishin shugaban kasar, ya ayyana dokar ta baci ta tsawon shekara guda, inda aka damkawa babban kwamandan manyan hafsoshin tsaron kasar, ikon kula da harkokin majalisa, da zartaswa da na shari’ar kasar.
Haka nan kuma sun sanar a wannan Litinin cewa, zasu shirya sabon zabe a kasar bayan kammala cikar wa’adin dokar ta bacin da suka kafa a kasar ta tsawon shekara guda, daga bisani zasu maido da iko ga sabuwar gwamnadin kasar da za a zaba.
A sanarwar da aka fitar ta gidan talabijin din kasar wanda sojojin suka karbe ikonsa, ance za a mika ragamar shugabancin kasar ga babban hafsan tsaro na kasar Myanmar, Min Aung Hlaing.