IQNA

Karfafa Tattaunawa Tsakanin Addinai Ita Ce Manufar Ziyarar Da Paparoma Zai Kai Kasar Iraki

23:05 - January 31, 2021
Lambar Labari: 3485607
Tehran IQNA) Paparoma Francis na da shirin gudanar da wata ziyara a kasar Iraki inda zai gana da manyan malaman addini na kasar.

A cikin wannan makon ne shugaban mabiya addinin kirista na darikar Katolika Paparoma Francis ya tabbatar da cewa yana da shirin gudanar da wata ziyara a kasar Iraki inda zai gana da babban malamin addini na kasar Ayatollah Sayyid Ali Sistani, da ma wasu daga malamai da jami’ai na kasar.

Wannan dai shi ne karon farko da babban malamin addinin kirista na darikar katolika zai kai ziyara a kasar Iraki domin ganawa da malaman addini na kasar, wanda tuni aka shirya gudanar da wannan ziyara, amma sakamakon barkewar cutar corona an yi ta dage tafiyar.

Kafin wannan lokacin dai Paparoma Francis ya yi tafiye-tafiye zuwa wasu daga cikin kasashen musulmi, kamar a 2014 ya tafi Falastinu da kuma Jordan, sannan ya je Turkiya da Azerbaijan a cikin wannan shekara,a cikin 2016 ya tafi Masar, sai kuma 2017 ya yi tafiya zuwa Bangaladesh, da hadaddiyar daular larabawa UAE, sai kuma a 2019 ya ziyarci Mrocco.

Ofishin Paparoma ya sanar da cewa, zai ziyarci Iraki ne a ranar 5 ga watan Maris mai zuwa, inda zai gana da Ayatollah Sistani da kuma wasu manyan malamai na kasar.

Babbar manufar ziyarar da Paparoma zai kai kasar Iraki ita ce, karfafa tattaunawa tsakanin addinai, domin yada zaman lafiya a duniya a tsakanin al’ummomi, tare da karfafa fahimtar jina da girmama mahanga da akidun juna.

3950747

 

 

captcha