Shafin yada labarai na Arabic 21 ya bayar da rahoton cewa, a safiyar yau jami’an tsaron gwamnatin yahudawan Isra’ila su kutsa kai a cikin yankunan Falastinawa da ke yankin Ummu Kissah.
Bayan nan kuma yahudawan sun shiga rusa ginin wani masallaci da ake cikin gina shi, kamar yadda kuma suka rusa wata makaranta mallakin Falastinawa da take kusa da masallacin tare da baje ta tare da masallacin.
Jami’an tsaron yahudawan Isra’ila dauke da makamai sun hana kowa isa wurin, tare da yin barazanar harbin duk wani musulmi da ya nemi isa wurin domin hana rusa wannan masallaci da makaranta.
Wannan yankin dai yana daga cikin yankuna mallakin Falastinawa wanda majalisar dinkin duniya ta amince da su a matsayin mallakinsu, wanda kuma yahudawa na ci gaba da rusa gidajen falastinawa a wadanann yankuna tare da mamaye su.