IQNA

Martanin Duniya Kan Farmakin Da Magoya Bayan Trump Suka Kaddamar Kan Majalisar Dokokin Amurka

19:58 - January 07, 2021
Lambar Labari: 3485531
Tehran (IQNA) duniya na ci gaba da yin tir da harin da magoya bayan shugaba mai barin gado na Amurka suka kai kan majalisar dokokin kasar.

Kasashen duniya na ci gaba da yin tir da harin da magoya bayan shugaba mai barin gado na Amurka suka kai kan majalisar dokokin kasar a lokacin da ‘yan majalisar kasar ke taro domin tabbatar da nasarar dan takarar jam’iyyar democrat Joe Biden.

Lamarin dai ya haifar da rikici tsakanin magoya bayan Trump, da kuma ‘yan sanda wanda ya haifar da tarzoma a ginin majalisar wato capitol a jiya Laraba.

Kasashen duniya da dama musamman manyan kawayen Amurka na turai, duk sun nuna jin takaici game da lamarin, wanda suka ce tamakar yi wa tsarin demokuradiyar Amurka karan tsaye ne.

Baya ga hakan manyan jami’an Amurka da ‘yan siyasa da kuma tsoffin shugabannin kasar irin su Bill Clinton, da Barack Obama duk sun yi tir da lamarin.

Shafukan sada zumunta na twitter da facebook, su ma sun dakatar da shafukan Trump na wani dan lokaci, saboda abin da suka kira karya dokokinsu.

Rahotanni daga kasar ta Amurka sun tabbatar da cewa, mutane 4 aka tabbatar da sun rasa rayukansu sakamakon tarzomar da magoya bayan Donald Trump suka tayar a cikin ginin majalisar dokokin kasar .

Bayanan da suke fitowa daga kasar ta Amurka dai na cewa, sakamakon farmakin da magoya bayan shugaban kasar ta Amurka mai barin gado Donald Trump, suka kai kan ginin majalisar dokokin, akalla mutane 4 ne suka rasa rayukansu.

Farmakin magoya bayan Trump dai ya tilasta majalisar dakatar da zaman da take gudanarwa dangane da sakamakon zabe, inda Trump din ya riga zuga su da kuma tunzura su domin su kawo cikas ga zaman, wanda ya yi imanin cewa za a tabbatar da Joe Biden a matsayin wanda ya lashen shugaban kasar da aka gudanar.

Daga bisani bayan da jami’an tsaro suka samu nasarar fitar da masu tarzomar, majalisar ta ci gaba da gudanar da zamanta.

Kungiyar tarayyar turai ta yi Allawadai da abin da ya faru, tare da bayyana hakan a matsayin keta hurumin dimukradiyya, tare da kira ga bangarorin da suka sha kayi a zaben da amince da shan kayin da suka yi, maimkaon tayar da tarzoma.

A nasa bangaren zababben shugaban kasar ta Amurka Joe Biden ya bayyana abin da yake faruwa da cewa, hari ne aka kaddamar kan dimukradiyyar Amurka.

Shugabannin kasashen arewaci da kudancin Amurka duk sun yi Allawadai da kakkausar murya kan abin da Doald Trump da magoya bayansa suka yi.

Sakamakon abin da ya faru a daren jiya, wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin sun yi murabus daga kan mukamansu domin nuna rashin amincewarsu da abin da ya aikata, daga ciki har da babbar sakatariyar hulda da jama’a ta fadar White House.

Tun bayan da kayin da Trump ya sha a zaben shugaban kasar da aka gudanar a cikin watan Nuwamban da ya gabata  akasar at Amurka, ya yi kememe tare da kin amincewa da sakamakon zaben, inda yake ikirarin cewa an yi magudi, wanda hakan yasa aka sake gudanar da kidayar kuri’u a wasu jihohin da yake shakku, amma duk da haka sakamakon dai bai canja ba.

3946245

 

captcha