IQNA

Tasirin Siyasar Kasashen Ketare A Cikin Nahiyar Afirka

20:29 - January 04, 2021
Lambar Labari: 3485522
Tehran (IQNA) sakamkaon yadda wasu daga cikin kasashe suke yin amfani da babban tasirinsu a kan siyasar duniya ko kuma masu amfani da kudi, wannan ya sanya tasirin wasu kasashe na samun wurin zama a Afirika.

A cikin shekarun baya-bayan nan an rika samun wasu kasashe da suke kutsa kai a cikin kasashen nahiyar Afirka, tare da yin amfani da hanyoyi daban-daban na samun wurin zama da sunan taimaka ma kasashen nahiyar da abubuwan da suke bukata.

Daga cikin irin wannan kutsen da aka samu a baya-bayan nan wando ya zo bayan kawo karshen mulkin mallaka a ksashen nahiyar Afirka, akwai kutse na kasashen yankin gabas ta tsakiya da kuma wasu kasashen Asia ta gabas.

Duk da cewa har yanzu kasashen da suka yi mulkin mallaka a kan kasashen nahiyar Afirka suna da nasu tasirin akan kasashe da dama da suka mulka, musamman Burtaniya da kuma Faransa, da kuma ‘yan mulkin mallakar siyas ada tattalin arziki kamar Amurka, duk suna da nasu tasirina kan kasashen Afirka.

To amma abin da ya zo daga bisani wanda ba da sunan mulkin mallaka ba, shi ne yafi yin tasiri, kamar kutse na addini da yada mahanga ta addini, wanda zai iya kasancewa ta hanyoyi daban-daban, amma abin da yafi saurin daukar hankali da yin tasiri shi ne yin amfani da makudan kudade wajen samar da mutane wadanda ke daukar nauyinsu domin hakan.

Sai kuma wani abu wanda ya shafi kasashe da ba addini ne a gabansu ba, harkokin kasuwancinsu ne muhimmi har kullum a gabansu, wadanda su ma suna samun tasiri a cikin kasashen nahiyar Afirka, daga cikin wadannan kasashen akwai Turkiya da kuma Sin da makamantansu.

3945404

 

 

 

captcha