IQNA

A Cikin Wani jawabinsa A Baya Jagoran juyin Iran Ya Jadda Cewa Za A Dauki Fansa Kan kisan Kasim Sulaimani

22:57 - December 27, 2020
Lambar Labari: 3485498
Tehran a cikin wani bayaninsa a lokutan baya jagoran juyin juya halin musluncia  Iran ya jadda cewa lallai za a dauki fansa kan kisan Kasim Sulamini

Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran ya bayyana kisan gillan da Amurkawa ta yi wa Kasim Sulaimani da Abu Mahdi Almuhandis  a matsayin ɗaya daga cikin munanan misalan kasantuwar Amurka a yankin Gabas ta tsakiya yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taɓa mantawa da wannan lamarin kuma ko shakka babu za ta mayar da martani makamancin hakan ga Amurkawa.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yayin ganawar da yayi da da firayi ministan ƙasar Iraƙi Mustafa Kazimi a ci gaba da ziyarar da ya ke yi a Iran inda Jagoran ya bayyana cewar alaƙar ta ke tsakanin Iran da Iraƙi wata tsohuwar alaƙa ce da ta samo asali sakamakon ababe da dama da ƙasashen biyu suka yi tarayya cikinsu, daga nan sai ya ce: Abin da ke da muhimmanci a wajen Iran cikin alaƙarta da ƙasar Iraƙi shi ne tabbatar da manufofi, tsaro, ɗaukaka, tabbatar da iko da kuma kyautatuwar yanayin da ƙasar Iraƙin take ciki.

Haka nan kuma yayin da ya ke bayanin cewa Iran dai ba ta tsoma baki cikin lamurran ƙasar Iraƙi kuma ba a nan gaba ma ba za ta tsoma ba, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Iran dai tana fatan ganin ƙasar Iraƙi ma'abociyar ɗaukaka, 'yancin kai da kuma tabbatar da ikonta a duk faɗin ƙasar bugu da ƙari kan tabbatar da haɗin kai tsakanin al'ummominta.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Ko shakka babu Iran tana adawa da duk wani abin da zai raunana gwamnatin ƙasar Iraƙi.

Ya ci gaba da cewa: Tabbas mahangar Amurkawa dangane da ƙasar Iraƙin ta yi hannun riga da mahangar mu, don kuwa ko shakka babu Amurka abokiyar gaba ce kuma ba ta maraba da ganin an samu ƙasar Iraƙi ma'abociyar ƙarfi da 'yancin kai da kuma gwamnatin da aka kafa ta bisa abin da mafiya yawan al'ummar ƙasar suke so.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Amurkawa ba su damu da waye zai zama firayi ministan Iraƙi ba. Abin da suke so shi ne gwamnati irin wacce Paul Bremer, tsohon shugaban da Amurka ta naɗa bayan kifar da gwamnatin Saddam.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ƙara da cewa: Iran dai ba ta tsoma baki dangane da alaƙar Iraƙi da Amurka, amma dai tana fatan ƙawayenta na Iraƙi za su fahimci wace ce Amurka da kuma cewa kasantuwar Amurka a wata ƙasa ba abin da zai haifar face lalata wannan ƙasar.

Ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana fatan za a ci gaba da bin diddigin matsayar da gwamnati, al'umma da kuma majalisar dokokin Iraƙi suka ɗauka na ficewar Amurkawa daga ƙasaar don kuwa ci gaba da zamansu ba abin da zai haifar face rashin tsaro.

Yayin da ya ke magana kan kisan gillan da Amurkawa suka yi wa Laftanar Janar Ƙasim Sulaimani (tsohon kwamandan rundunar Ƙudus ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci na ƙasar Iran) da kuma Abu Mahadi Al-Muhandis (tsohon mataimakin kwamandan dakarun sa kai na ƙasar Iraƙi) a ƙasar Iraƙ, Jagoran ya bayyana hakan a matsayin ɗaya daga cikin mummunan sakamakon kasantuwar Amurkawa a ƙasar Iraƙin. Daga nan sai ya ce wa firayi ministan Iraƙin: "Sun kashe baƙonku a cikin ƙasar ku sannan kuma a fili suka ɗauki alhakin hakan, lalle wannan ba ƙaramin abu ba ne".

Ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran har abada ba za ta taɓa mantawa da wannan lamarin ba, sannan kuma ko shakka babu za ta mayar wa Amurkawa da martani irin wannan.

Ya bayyana yadda bakin ƙungiyoyi da jam'iyyun siyasa daban-daban na ƙasar Iraƙin ya zo ɗaya wajen zaɓar gwamnatin Mustafa Kazimin a matsayin wani lamari abin yabawa, daga nan sai ya ce: "Amurkawa da 'yan amshin shatansu a ko da yaushe suna fatan ganin an samu matsalar shugabanci a ƙasashen yankin Gabas ta tsakiya don ta hanyar wannan rikicin za su sami damar tsoma bakinsu cikin harkokin cikin gidajen waɗannan ƙasashen. Wannan shi ne abin da suka yi a Yemen, kamar yadda a halin yanzu kowa ya ke ganin irin halin tsaka mai wuyan da ake ciki a Yemen.

Haka nan kuma yayin a ya ke jaddada goyon bayan Iran ga gwamnatin Mustafa Kazimin, Jagoran ya bayyana cewar: "Hankali, addini da kuma ƙwarewar da ake da ita sun tabbatar da wajibcin yin ƙoƙari wajen ganin an ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin Iran da Iraƙi a dukkan ɓangarori.

Jagoran ya ce: "Ko da yake akwai wasu da suke adawa da ƙarfafa alaƙa tsakanin Iran da Iraƙin wanda Amurka ce a kan gabansu, to sai dai bai kamata a ji tsoron Amurka ba don kuwa babu wani abin da za ta iya yi.

Ya ci gaba da cewa: Tabbas Amurkawa za su haifar da matsaloli, to amma dole ne gwamnatin Iraƙi ta ci gaba da tafiya bisa tafarkin da ta zaɓa ba tare da la'akari da waɗannan matsalolin da Amurkan za ta haifar ba. Kamar yadda kuma wajibi ne ta kare al'ummarta waɗanda su ne ƙarfinta.

Jagoran ya bayyana kasantuwar marja'iyya musamman Ayatullah Sistani a matsayin wata babbar ni'ima ga ƙasar Iraƙi daga nan sai ya ce: (Dakarun sa kai) na Hash al-Sha'abi su ma wata ni'ima ce babba ga Iraƙin da wajibi ne a kiyaye su.

Shi ma a nasa ɓangaren, firayi ministan ƙasar Iraƙin, Mustafa Kazimi, wanda mataimakin shugaban ƙasar Iran na farko Ishaƙ Jihangiri ya ke wa rakiya, ya bayyana ganawa da Ayatullah Khamenei a matsayin wata babbar dama kana abin farin ciki a gare shi, sannan kuma yayin da yake nuna godiya da kuma jinjinawa ga Iran saboda irin goyon bayan da take ba wa ƙasar Iraƙi musamman a lokacin faɗa da 'yan ƙungiyar ta'addancin nan ta Daesh da sauran 'yan takfiriyya, firayi ministan Iraƙin ya ce: Har abada al'ummar Iraƙi ba za su taɓa mantawa da irin goyon bayan da Iran take ba su ba.

Firayi ministan Iraƙin ya shaida wa Jagoran cewa: "Shiryawa da kuma nasihohinka sun zamanto wani mabuɗi na magance matsaloli, kuma lalle ina godiya da irin waɗannan nasihohi da shiryarwa".

3943265

 

captcha