IQNA

Kawance Na Ci Gaba Da Kara Kankama Tsakanin Isra'ila Da Saudiyya

23:59 - February 25, 2020
Lambar Labari: 3484560
Ana ci gaba da kara samun karfafar kawance tsakanin masarautar Saudiyya da gwamnatin yahudawan Isra'ila.

Da dama daga cikin kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton cewa, a cikin makon da ya gabata wani babban malamin yahudawan Isra’ila ya ziyarci fadar sarkin Saudiyya a birnin Riyad fadar mulkin kasar.

Daya daga cikin manyan jaridun yahudawa a cikin rahoton da ta bayar a yau  jaridar Times of Israel ta bayyana cewa, a makon da ya gabata David Ruzan daya daga cikin majalisar koli ta malaman yahudawan Isra’ila ya ziyarci kasar Saudiyya, a cikin wata tawaga da sunanan tattaunawar addinai a kasar.

A cikin rahotan nata jaridar ta ce bayan dawowarsa, malamin yahudawan ya sheda wa kafofin yada labaran Isra’ila cewa lallai tafiyarsa zuwa Saudiyya ta yi armashi matuka, domin kuwa ya gana da sarkin saudiyya a fadarsa da ke Riyad, kuma ya samu kyakkyawar tarba daga sarki dama jami'an masarautar.

Haka nan kuma ya ce duk wannan ma ba shi ne yake da muhimmanci ba, ganawarsa da matasa a kasar saudiyya ita ce tafi muhimmanci, domin kuwa ya fahimci akwai gagarumin sauyi a tattare da tunanin matasan kasar daga irin maganganun da suka yi a ganawarsu da shi inda ya sha mamaki kan yadda aka samu sauyi a tunaninsu kan yahudawa.

Rahotanni daga tashoshin yada labaran Isra'ila sun ko a farkon wannan wata na Fabrariru wasu shugabannin manyan kungiyoyin yahudawa daga Amurka sun ziyarci Saudiyya, inda suka gana da sarakunan kasar kan abubuwa da dama wadanda ba a bayyana su ba amma dai suna da alaka da habbaka dangantaka tsakanin masarautar da kuma gwamnatin yahudawa.

3878443

 

captcha