Kafar labarai ta kasar Masar Alyaum Sabi ta bayar da rahoton mutuwar Husni Mubarak a rahotanninsu na yau Talata.
Babban dansa Ala Mubarak ya sanar da cewa an yi wa mahaifinsa aikin tiyata a daya daga cikin asibitocin birnin Alkahira tun a cikin watan Janairu.
Haka nan kuma Ala ya bayyana cewa, mahaifinsa yana kwance a dakin kulawa ta musamman tun bayan yi masa aikin tiyataa asibiti.