IQNA

​Buhari: Kwanakin Boko Haram Sun Zo Karshe

21:42 - February 25, 2020
Lambar Labari: 3484557
Tehran (IQNA)_Shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ya bayyana cewa ana shirin kaddamar da wasu munanan hare-hare kan mayakan kungiyar Boko haram, wanda hakan zai kawo karshenta baki daya

Wannan furuci dai ya zo ne sakamakon yadda ake ci gaba da nuna damuwa kan yadda mayakan kungiyar suke ta kara zafafa hare-harensua cikin lokutnanan, musamman a yankunan arewa maso gabashin kasar.

Mai Magana da yawun shugaba Buhari wato Garba Shehu, yabbana cewa shugaban ya damu matuka da irin zubar da jinin al’umma da masu tayar da kayar bayan ke yi, a kan haka bangarorin tsaro na kasar suna wani shiri na kaddamar da wani farmaki nan da ‘yan makonni masu zuwa, wanda shi ne mafi girma, kuma shi ne zai kawo karshen kungiyar Boko haram.

Haka nan kuma Buhari ya bayyana cewa, hare-haren da mayakan kungiyar suke kaiwa a wasu yankuna da babu tsaro sosai da cewa, hakan ba komai ba ne illa farfaganda, domin boye irin raunin da kungiyar ta yi ne.

http://ha.hausatv.com

captcha