IQNA

Martanin Falastinawa 'yan Gwagwarmaya A Kan Matsugunnan yahudawa

23:56 - February 24, 2020
Lambar Labari: 3484556
Tehran (IQNA) falastinawa 'yan gwagwarmaya sun sanar da mayar da martani kan hare-haren da Isra'ila ta kaddamar a kansu.

A wata sanarwa da dakarun “Sarayal-Quds’ su ka fitar sun bayyana cewa; Sun kai harin ne a amstayin mayar da martani ga kisan gillar da sojojin sahayoniya su ka yi wa daya daga cikin mayakansu Muhammad al-Na’im, da kuma wulakanta gawarsa.

Dakarun na “Sarayal Quds” sun kai harin ne akan matsugunin ‘yan share wuri zauna dake Asqalan a kusa da sansanin Gaza.

Da safiyar yau Litinin ne dai dakarun na Sarayal Qudus su ka sanar da shahadar Muhammad Ali Hassan al-Na’im, wanda ‘yan sahayoniya su ka kashe a garin Khanyunus a jiya Lahadi.

Haka nan kumakungiyoyin falastinawa 'yan gwagwarmaya sun sha alwashin daukar dukkanin matakan da suka dace omin kare al'ummarsu daga duk wani matakin yin shishigi kan su dangangaren yahudawan sahyuniya.

 

3881214

 

captcha