IQNA

An Rufe Haramin Birnin Najaf Saboda Coronavirus

23:03 - February 24, 2020
Lambar Labari: 3484555
Tehran - (IQNA) an rufe haramin birnin Najaf sakamakon yaduwar cutar corona a kasashen yankin gabas ta tsakiya.

Rahotanni daga birnin Najaf na Iraki sun ce an rufe hubbaren Imam Ali (AS) domin daukar matakai na hana yaduwar cutar nan ta coronavirus a tsakanin masu ziyara.

Bayanin ya ce an dauki wannan matakin ne daga yau har zuwa wani lokaci nan gaba da ba a bayyana ba, domin samun damar yin feshi da kuma kula da wurin domin lafiyar al'umma.

Cutar dai ta yadu a cikin wasu daga cikin kasashen da suke makwaftaka da Iraki, wadanda suna zuwa ziyara a kasar, wanda hakan ka iya jaza bullarta  cikin kasar.

 

3881216

 

 

captcha