IQNA

Mahatir Muhammad Ya Yi Murabus Daga kan Mukaminsa

22:59 - February 24, 2020
Lambar Labari: 3484554
Tehran - (IQNA) firayi ministan kasar Malaysia Mahatir Muhammad ya yi murabus daga kan mukaminsa a yau.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a yau firayi ministan kasar Malaysia Matir Muhammad ya yi murabus daga kan mukaminsa, lamarin da ya jefa kasar cikin wani halai na dambarwar siyasa.

Bayanin ya ce Mahatir ya mika takardar murabus dinsa ga sarkin kasar ta Malaysia, wanda shi ne zai duba ya ga matakin da ya dace a gaba.

Ana hasashen cewa Mahatir ya dauki wannan mataki ne sakamakon sabanin da ke tsakaninsa da kuma magajinsa Anwar Ibrahim, wanda kuma shi ne babban abokin kawancesa da suka hada gwamnati tare.

Ko a jiya Lahadi Anwar Ibrahim ya yi zargin cewa, jam'iyyar Matir da kuma wasu daga cikin 'yan jam'iyyarsa suna da nufin ballewa domin kafa wani kawancen na daban, da nufin kafa wata hukumar wadda babu jam'iyyarsa a ciki.

Mahatir Muhammad dan shekaru 94 yana da karbuwa a wajen mutanen kasar Malaysia, kamar yadda kuma ya shahara a duniya wajen nuna tsananin adawa da salon siyasar danniya irin ta Amurka da sauran 'yan mulkin mallaka.

 

3881152

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Mahatir malaysia murabus daga mukami yau
captcha