IQNA

An sake Dage sauraren Shari'ar Sheikh Zakzaky da Mai Dakinsa

22:57 - February 24, 2020
Lambar Labari: 3484553
Kotun kaduna ta sake dage sauraren shari'ar sheikh Ibrahim zakzaky da mai dakinsa malama Zinat.

Majiyoyin harkar muslunci a Najeriya sun ce a yau kotun da ke sauraren shari'ar sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran Harakar Musulunci da mai dakinsa malama Zint ta zauna a birnin Kaduna.

A yayin zaman dai sheikh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa da kuma lauyoyinsu gami da lauyoyin gwamnati sun samu halarta.

A yayin zaman lauyoyin sheikh Zakzaky sun gabatar da korafi kan hana likitocinsa yi masa magani a inda ake tsare da sua  cikin kurkukun Kaduna.

Amma a nasu bangaren lauyoyin gwamnati sun musunta hakan, wanda hakan yasa alkalin ya bayar da umarni kan cewa dole ne shugaban gidan yarin ya halarci wurin domin jin bahasi daga bakinsa.

Bayan tattaunawa tsakanin dukkanin bangarorin, an cimma matsaya kan cewa likikitan sheikh Zakzaky ne zai rika duba shi a inda ake tsare da shi tare da halartar likitoci na wurin da kuma na gwamnati.

Haka nan kuma alkalin ya dage shari'ar zuwa makon karshe na watan Afirilun wannan shekara. 

 

3881221

 

captcha