IQNA

Rauhani: Takunkumin Amurka Ya Yi Kama Da Corona Tsoron Kamuwa Da Shi Ya Fi Hadarinsa Yawa

23:55 - February 23, 2020
Lambar Labari: 3484551
Tehran - (IQNA) shugaban kasar Iran ya bayyana cewa Amurka tana barazana da takunkumi amma kuma sau da yawa ya kan zama dama ga kasashe domin dogara da kansu.

Shugaban kasar Iran Hassan Rauhani ya gana da ministan harkokin wajen kasar Austria Alexander Schallenberg a yau a fadarsa da ke birnin Tehran.

A yayin ganawar, shugaba Rauhani ya bayyana cewa, kasashen Iran da Austria suna da alaka ta tarihi, wadda ta ginu a kan girmama jina da kuma yin mu’amala da juna a bangarori daban-daban na ci gaba a tsakanin kasashen biyu.

Ya ce babban abin takaici ne yadda wasu kasashe suka dauki salon siyasar kakaba takunkumi kan wasu kasashe a halin yanzu saboda dalilai na siyasa, wanda hakan ya zama shi ne siyasar Amurka a yanzu, matukar wata kasa bat a mika wuya ga manufifin siyasarta ba, to za ta kakaba mata takunkumi, wanda hakan a cewar Rauhani ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa.

Ya ci gaba da cewa, dangane da batun yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, bayan ficewar Amurka daga yarjejeniyar kasashen turai ba su cika alkawullan da suka dauka wa Iran ba, a kan haka Iran za ta ci gaba da mutunta wannan yarjejeniyar ne kawai daidai da yadda su ma suka mutunta ta.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen Austria Alexander Schallenberg , ya bayyana cewa, kasarsa tana nan kan bakanta na mutunta yarjejeniyar nukiliya tsakanin Iran da kasashen duniya, kamar yadda kuma alaka tsakanin kasashen biyu tana nan daram.

 

https://iqna.ir/fa/news/3880891

captcha