IQNA

Gasar Kur’ani Ta Kasa A Gidan Talabijin Din Morocco

22:59 - February 22, 2020
Lambar Labari: 3484548
Tehran – (IQNA) an fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa wadda ake gudanarwa  agidan talabijin na kasa kai tsaye a Maorocco.

Rahotanni daga kasar Morocco sun habarta cewa, a jiya ne aka fara fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa wadda ake gudanarwa  a gidan talabijin na kasa kai tsaye tare da halartar makaranta da mahardata daga sassa na kasar.

Bayanin ya ce yara tsakanin shekaru 10 zuwa ne suke halartar gasar, wadda kuma wannan shi ne karo na goma sha bakawai da ake gudanar da irin wannan gasa a kasar.

Daga karshe za a bayar da kyautuka na musamman ga dukaknin wadanda suka nuna kwazo, kuam daga wanann gasar ne ake zabar wadanda za su wakilci kasara gasar kur’ani ta duniya.

 

3880534

 

 

 

 

captcha