IQNA

Wani Kasurgumin Bayahuden Isra'ila A Fadar Sarkin Saudiyya

23:58 - February 21, 2020
Lambar Labari: 3484547
Tehran - (IQNA) a karon farko a bainar jama'a daya daga cikin manyan malaman yahudawan Isra'ila masu tsatsauran ra'ayin yahudanci ya halarci fadar sarkin Saudiyya.

Shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, a jiya Alhamis sarkin masarautar 'ya'yan Saud Salman Bin Abdulaziz ya tarbi Khakham David Ruzan, daya daga cikin manyan malaman yahudawan Isra'ila a fadarsa da ke birnin Riyad, wanda shi ne karin farko da aka taba ganin haka a bayyane.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun yi ta yada wannan labari, tare da bayyana shi amatsayin gagarumin ci gaban da aka samu na alaka tsakain Saudiyya da gwamnatin yahudawan Isra'ila.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila take hankoron mamaye sauran yankunan falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan da kuma gabashin birnin quds.

Ko a karshen watan Janairun da ya gabata, Aryeh Deri ministan harkokin cikin gida na gwamnatin yahudawan Isra'ila ya bayyana cewa, sun cimma matsaya tare da mahukuntan Saudiyya kan bayar da dama ga yahudawan Isra'ila da su shiga Saudiyya domin gudanar da harkokinsu, kuma masarautar kasar ta amince da hakan.

 

3880238

 

 

captcha