IQNA

Jagora: Duk Wanda Ya Damu Maslahar Kasa To Ya Fito Ya Kada Kuri’a

23:55 - February 21, 2020
Lambar Labari: 3484545
Tehran – (IQNA) a lokacin da ya kada kuri’arsa a safiyar yau, jagoran juyin juya halin mulsunci a Iran ya kirayi jama’a da su fito domin kada nasu kuri’un.

Da sanyin safiyar yau Juma’a ne aka fara kada kuri’a a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar gami dana ‘yan majalisar kwararu ta musulinci.

A lokacin da ya kada kuri’arsa jagoran juyin juya halin musulinci na kasar, Ayatollah Khamenei, ya ce zabe ‘yanci ne kuma shi ne muradin kasa, kafin daga bisani ya yi kira ga al’ummar kasar da su fito dafifi domin kada kuri’a.

Wannan dai shi ne zaben ‘yan majalisar dokoki na sha daya a Iran, inda ‘yan takara kimanin dubu bakwai da dari da hamsin ke zawarcin kujerun majalisar dokokin kasar 290, a wani wa’adi na shekaru hudu.

‘Yan kasar ta Iran, miliyan hamsin da bakwai da dubu dari tara da goma sha takwas da dari da hamsin da tara ne suka tantanci kada kuri’a a zaben na yau.

Haka kuma a yayin zaben Iraniyawan zasu zabi wadanda zasu maye gurbin wakilan majalisar kwararu masu zaben jagora a kasar wadanda suka rasu, wacce ita ce ke nada jagoran juyin juya halin kasar a lokacin da bukatar yin hakan ta taso.

 

3880212

 

 

captcha