IQNA

Wani Musulmi Dan Kasar Argentina Na Kokarin Yada Addinin Musulunci A Kasar

23:58 - February 20, 2020
Lambar Labari: 3484544
Tehran (IQNA) wani musulmi dan kasar Argentina na kokarin yada addinin musulunci a kasar da ma yankin latin.

Edgardo Robin As’ad musulmi ne dan kasar Argentina, wanda a zantawarwa da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayyana cewa, ya kwashe tsawon shekaru yana gudanar da ayyuka daban-daban na isar da sakon addinin muslunci a kasar Argentina.

Ya ce bisa la’akari da yanayin kasarsu, dole ne ya yi amfani da hanyoyi na hikima wajen isar da abin yake son isarwa ga jama’a, musamman ganin cewa ba kasa ce ta musulmi ba.

As’ad ya ce ya yi tafiye-tafiye masu yawa a kasashen duniya da suka hada da kasashen musulmi, kuma yana da dangantaka da cibiyoyi daban-daban na kasashen musulmi.

Ya ce aiki a irin wannan yana da wuya, yana bukatar hakuri da kuma dagewa domin kaiwa ga manufa, manufar kuma ita ce isar sa hakikanin sakon muslunci ga mutanen da ba su ma san mene ne addinin muslunci ba, maimakon haka ma suna daukar addinin muslunci wani addini na zamanin da wanda babu komai a cikinsa kisa da tashin hankali da ta’addanci.

 

 

3879891

 

 

captcha