IQNA

Zaman Tarayyar Turai Domin Tattauna Batun Yarjejeniyar Karni

23:58 - February 16, 2020
Lambar Labari: 3484529
Tehran – IQNA, kungiyar tarayyar turai za ta gudanar da zama dimin tattauna batun shirin Trump kan Falastinu da ake kira yarjejeniyar karni.

Kamfanin  dillancin labaran Falastinu na safa ya bayar da rahoton cewa, ministocin harkokin wajen kasashe mambobi a kunfiyar tarayyar turai ne za su gudanar da zaman a gobe Litinin, inda za su yi dubi kan shirin na Trump.

Tun kafin wannan lokacin dai kungiyar tarayyar turai ta bayyana matsayinta na kin amincewa da shirin na Trump, tae da bayyana cewa yana da tawaya, domin kuwa ya shafi bangare daya ne kawai wato Isra’ila, ba tare da ya hada bangaren falastinawa ba.

Kungiyar tarayyar turai ta bayyana cewa duk wani shirin samar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falastinawa, to dole ne ya hada dukkanin bangarorin biyu, kuma duk abin da za a aiwatar ya zama bisa amincewar dukkanin bangarorin biyu ne.

A daya bangaren kuma wasu mazauna birnin Prague fadar mulkin kasar Zchech sun gudanar da gangami a gaban ofishin jakadancin Amurka da ke birnin, tare da nuna rashin amincewa da shirin na Trump, wanda suke bayyana shi a matsayin wani sabon zalunci a kan al’ummar falastinu.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3879130

captcha