IQNA

Kamfanoni Masu Gina Matsugunnan Yahudawa Ayyukansu Sun Saba Wa Doka

20:58 - February 13, 2020
Lambar Labari: 3484519
Majalisar dinkin dinkin dniya ta ayyana wasu kamfanoni masu aikin gina matsugunnan yahudawa a Falastinu da cewa aikinsu ba halastacce ba ne.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, majalisar dinkin duniya ta saka kamfanoni 112 da suke yi Isra’ila aikin gina matsugunnan yahudawa a cikin yankunan falastinawa a cikin kamfanonin da suka saba wa doka.

Daga cikin wadannan kamfanoni 112 da suke gina matsugunnan yahudawa a cikin yankunan falastinawa, 94 suna aiki ne kawai a cikin yankunan falastunawa da Isra’ila ta mamaye, yayin da 18 suna yin ayyuka a kasashe 6 na duniya.

Haka nan kuma bayanin ofishin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa, 95 daga cikin kamfanonin na Isra’ila ne, 6 kuam na Amurka, 4 na Holland, 3 na faransa, 2 na Burtaniya, 1 na Thailand, sai kuam wani 1 na Luxumburg.

Majalisar dinkin duniya da kungiyar tarayyar turai sun bayyana ayyukan mamayar yankunan falastinawa da Isra’ila take yi da cewa ya ya saba wa ka’ida, kuma matsugunnan yahudawan da ake ginawa a cikin wadannan yankuna ba su da halasci.

 

https://iqna.ir/fa/news/3878508

 

captcha