IQNA

Sayyid Narullah: Saka IRGC Cikin ‘yan Ta’adda Alama Gazawa Ce daga Amrka

23:59 - April 10, 2019
Lambar Labari: 3483538
Bagaren kasa da kasa, Sayyid nasrullah ya bayyana saka dakaun kare juyin juya halin muslucni cikin wadanda Amurka ke kira ‘yan ta’adda da cewa babbar gazawa ce daga Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewa sanya dakarun kare juyin Musulunci na kasar Iran (IRGC) cikin kungiyoyin ta’addanci da Amurka ta yi, wani lamari ne da ke nuni da cewa Amurka ta gaba cimma bakaken aniyarta a yankin Gaskiya.

Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a yammacin jiya Laraba don tunawa da ranar wadanda suka sami raunuka a fagen daga, inda yayin da yake magana kan sanya dakarun IRGC din cikin kungiyoyin ta’addanci da Amurka ta yi yace hakan wata alama ce da take nuni da cewa Amurkan tana cikin tsaka mai wuya a yankin Gabas ta tsakiya.

Shugaban kungiyar ta Hizbullah ya ci gaba da cewa: Dakarun IRGC din sun yi tsayin daka da kuma sadaukarwa mai girma wajen hana Amurka da HKI cimma bakar aniyarsu a yankin nan, don haka yace suna yin Allah wadai da wannan mataki na Amurka kamar yadda kuma ya sake jaddada goyon bayansa da dakarun na IRGC.

A ranar Litinin din da ta gabata ce shugaban Amurkan Donald Trump ya sanar da matsayar gwamnatinsa na sanya dakarun na IRGC cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda lamarin da Iran ta yi Allah wadai da shi, sannan al’ummar kasar kuma suka sake jaddada goyon bayansu ga dakarun na IRGC.

3802751

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha