IQNA

Za A Aike Da Abincin Halal Zuwa Sararin Samaniya

23:48 - July 07, 2019
1
Lambar Labari: 3483814
Bangaren kasa da kasa, wani kamfanin abinci a kasar Rasha zai aike da abincin halal zuwa sararin samaniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar rahoton cewa, Huza Ali Amnasuri dan kasar hadaddiyar daular larabawa UAE, na shirin tafiya zuwa sararin samaniya a cikin watan Satumba mai zuwa.

Kasantuwar wannan mutum musulmi ne, wani kamfani mai suna Space Food Laboratary ya shirya abinci na musamman wanda wannan mutum zai yi amfani da shia  sararin samaniya.

A cikin shekara ta 2018 ce hadadiyar daular larabawa ta kulla wata yarjejeniya tare da Rasha kan zuwa sararin samaniya.

Amansuri tare da wani mutum mai suna Sultan Niyadi dukkaninsu ‘yan kasar hadaddiyar daular larabawa, su ne suka bukaci tafiya zuwa sararin samaniya.

Tuna  cikin shekarar da ta gabata ne suka samu horo na zuwa sama, amma Almansuri ne shi ne ya samu sa’ar dacewa, inda zai yi kwanaki takwas a sama kafin ya dawo kasa.

 

3825013

 

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
ABDULRAHMAN SHUAIB
0
0
Nima ina sha'awar zuwa sararin samaniya_ kuma ina sha'awar ilimin kimiyya. da bincike a sararin samaniya... nifa inaso naje duniyar MARS_JUPITER_VENUS nagode!
captcha