IQNA

Shugaban masar Ya Hana Sheikhul Azhar Fita Sai Da Izininsa

20:45 - January 17, 2019
Lambar Labari: 3483322
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Masar Abdulfattah Sisi ya hana babban malamin Azhar fita daga Masarsai da izininsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shugaban kasar Masar Abdul Fattah Assisi ya bada umurnin kan cewa babu wani babban jami'an gwamnatin kasar da zai sake yin tafiya zuwa kasashen waje ba tare da izinin sa ba, daga ciki har da Shugaban Jami'an Al-Azhar.

Dokar ta bayyana cewa jami'an gwamnatin da abin ya shafa sun kama daga Firai Minister, mataimakinsa da sauran manya-manyan shuwagabannin ma'aikatun gwamnati ba zau yi wata tafiya zuwa kasashen waje ba sai tare da izinin fadar shugaban kasa.

Jaridar ta kara da cewa wannan umurnin ya hada har da shugaban Jami'an Al-azhar Shiek Ahmad Attayyib, duk da cewa jami'an al-azhar ba kai tsaye take karban umurni daga gwamnatin shugaba assisi ba. 

Wasu kafafen sadanarwa na yanar gizo sun yi allawadai da wannan umurnin, suna kuma ganin cewa wannan wani kokari ne na shugaba Abdulfattah Assisi na shimfida ikonsa a kan ma'aikatun gwamnati da masu zaman kansu.

3782047

 

 

 

captcha