IQNA

Ansarullah: Manzon Majalaisar Dinkin Duniya Ya Kasa Aiwatar Da Aikinsa

22:08 - January 13, 2019
Lambar Labari: 3483313
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta zargi manzon musamman na mjalisar dinkin duniya mai shiga tsakani kan rikicin Yemen da kasa aiwatar da aikinsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Sputnik ya bayar da rahoton cewa, mai magana da yawun kungiyar Ansarullah a Yemen Muhammad Abdulsalam ya zargi manzon musamman na mjalisar dinkin duniya mai shiga tsakani kan rikicin Yemen Matin Griffiths da kasa tabbatar da cewa dukkanin bangarori sun yi da yarjejeniyar da aka cimmawa.

Ya ce tun bayan da aka cimma yarjeneiyar dakatar da bude wuta har yanzu Saudiyya da sojojin hayarta ba su yi aiki da abin da yarjejeniyar ta kunsa ba, domin kuwa abin yake faruwa a Hudaidah ya kara tabbatar dahakan, inda suke cin karensu babu babbaka a gaban jami’an majalisar dinkin duniya, suna kai hare-hare da jiragen yaki kan gidajen jama’a suna kashe fararen hula.

Ya ce idan har sauran bangarorin yarjejeniyar ba su aiki da ita ba, to ba wajibi ne kan kungiyar ta Ansarulla su yi aiki da yarjejeniyar, kuma alhakin hakan yana kan manzon majalisar dinkin duniya ne.

3780846

 

 

 

captcha