IQNA

Sakataren harkokin wajen Amurka Ya kai Ziyarar ba Zata A Iraki

22:52 - January 09, 2019
Lambar Labari: 3483301
Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya isa a birnin Bagadaza na kasar Iraki, a wata ziyarar ba zata inda ya gana da wasu manyan jami'an kasar ta Iraki ciki harda shugaban majalisar dokoki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wanann ziyarar ita ce ta biyu a ran gadin da babban jami'in harkokin wajem Amurka ya fara yankin, bayan da ya ziyarci kasar Jodan a jiya.

Kuma ziyarar ziyarar sakataren harkokin wajen na Amurka a Iraki, na zuwa ne kasa da mako biyu bayan da shugaban kasar, Donald Trump, ya kai wata ziyara ga sojojin Amurka dake jibge a Iraki.

Ziayar da Trump ya kai ba tare da sanin hukumomin Irakin ba, ta fuskanci suka sosai, inda babu wata ganawa da mahukunatan kasashen sukayi a yayin ziyarar ta Trump.

Ko baya ga kasashen Jodan da Iraki, sakataren harkokin wajen na AMurka, zai ziyarci kasashen Masar, Bahrain, da hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya da Oman da kuma Koweit.

3779933

 

 

 

 

captcha