IQNA

Dadaddun Tafsiran Kur’ani A Kasar Mauritania

21:07 - January 06, 2019
Lambar Labari: 3483288
Bangaren kasa da kasa, dakin karatu na birnin Walata a kasar Mauritania yana da tafsiran kur’ani mai tsarki guda 2500 da aka rubuta da hannu tun daruruwan shekaru.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Alarabi Jadid ya habarta cewa, wannan dakin karatu da ke a garin tarihi na Walata mai tazarar kilo mita 1300 daga kudu maso gabashin birnin Nuwakshot, yana daga cikin dakunan karatu masu matukar muhimmanci a halin yanzu a nahiyar Afrika baki daya.

Rahoton yace tafsiran kur’ani da ke cikin wurin mafi yawa an rubuta su ne tun a cikin karni na biyar hijira kamariya, fiye da shekaru dari tara da suka gabata.

An gina wannan dakin karatu nea cikin shekarar 1990 tare da taimakon masu bincike na kasar Spain, inda aka harhadalittafai masu kima a cikinsa, kuma a halin yanzu, wani bangarensa ya zama wajen ajiye muhimman kayan tarihin musulunci.

Haka nan kuma yanzu wurin ya zama wurin da masu yawon bude ido da kuma masu bincike suke zuwa a kowace rana.

3778822

 

 

 

 

 

captcha