IQNA

A Sakonsa Na Kirsimati:

Paparoma Ya Kira kan Karfafa Zaman Lafiya Da Taimakon Marassa Galihu

23:54 - December 25, 2018
Lambar Labari: 3483251
Bangaren kasa da kasa, paparoma Francis jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katolika ya gabatar da jawabin kirsimati na wannan shekara.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin paparoma Francis jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katolika yake gabatar da jawabin nasa na bukukuwan kirsimati na wannan shekara a jiya afadar Vatican, ya yi ga jama’a da su zama masu daukar rayuwa mafi sauki.

Ya ce Almasihu ya rayu ne a cikin talakawa tun yana karami, saboda haka rayuwarsa rayuwa ce ta talakawa ba rayuwar masu kudi da jin dadi na duniya ba, kuma duk mai koyi da shi dole ne ya zama yana taka tsatsan a cikin lamarin jin dadin duniya.

Haka nan kuma ya yi ishara da wajabcin taimaka ma marassa galihu a duk inda suke a duniya, musamman yara wadanda ba su da masu taimako da kuma daukar nauyinsu.

3775456

 

 

 

captcha