IQNA

An Tarjama Fim Din Wilayar Eshq A Senegal

20:33 - July 21, 2018
Lambar Labari: 3482839
Bangaren kasa da kasa, an tarjama fim din wilayat Eshq a cikin harsunan kasar Senegal.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bisa himmar karamin ofishin jakadancin Iran a Dakar, an tarjama fim din wilayat Eshq a cikin harsunan kasar Senegal a daidai lokacin tunawa da zagayowar haihuwar Imam Ali bin Musa Redha (AS) wanda aka tarjama  acikin Harsunan Faransanci da Wolf.

Hassan Chao wanda dalibin digiri na uku ne a harshen farisanci a jami’ar Modarres shi ne yake gudanar da aikin tarjamar, wanda ya samu gudunmawa wajen samar da kayar aikin tarjamar daga jami’ar Antadiuop da ke birnin na Dakar tare da taimakon Aisha Jah babbar jami’a a bangaren shirya fima-finan kasa.

3731794

 

 

 

 

captcha