IQNA

Bunkasa Harkokin Otel Na Halal A Tunisia

23:59 - July 12, 2018
Lambar Labari: 3482830
Bangaren kasa da kasa, ana kara fadada ayyukan otel na halal a kasar Tunisia domin masu yawon bude ido musulmi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-amarat 71 cewa, a halin yanzu an kara fadada ayyukan otel na halal a kasar Tunisia domin masu yawon bude ido musulmi da duk mai bukata, bisa tsarin da kungiyar Nahda da Rashid Hanushi ta bullo da shi.

Balal Saffar mai otel Sandra Club shi ne ya kafa wani katafaren otel na halal, wanda a cikin an hana shan giya da aikata duk wani abin da ya saba wa addinin musulunci.

Haka nan kuma ana kiyaye tsarin zaman jama’a a wurin ta yadda mata da maza ba za su zauna wuri day aba, matukar dai ba mauarata ba ne.

Ya ce wannan tsari zai bayar da dama ga masu bukatar kiyaye lamurra na muuslunci su samu irin wurin da suke bukata domin yawon bude idi akasar ba tare da saba wa addinin suba.

3729368

 

 

 

captcha