IQNA

Wani Shirin Bada Horo Na Hardar Kur’ani Ga Yara Masar

23:52 - July 12, 2018
Lambar Labari: 3482827
Bangaren kasa da kasa, an bullo da wani shirin bayar da horo ga yara na kan hardar kur’ani a lardin Jiza na Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wannan makon an fara wani shirin bayar da horo ga yara 60 na kan hardar kur’ani a lardin Jiza na Masar da nufin yin amfani da hotun bazara domin hardar kur’ani.

A bisa yadda aka tsara a kowace rana yaran za su hardace shafuka goma daga kur’ani mai tsarki.

A cikin watanni biyu da za a kwase ana gudanar da shirin yaran za su iya hardace surori masu yawa daga kur’ani, wasu ma za su iya hardace kur’anin ya danganta da kwazon yaro.

3729413

 

 

 

 

captcha