IQNA

Firayi Ministan Somalia Ya Sauke Ministan Kula Da Harkokin Addini

22:46 - July 11, 2018
Lambar Labari: 3482824
Bangaren kasa da kasa, Firayi ministan kasar Somalia Ali Khairi ya sauke ministan ma’aikatar kula da harokin addini ta kasar Hassan Mu’allim Hussain.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ministan yada labarai na kasar Somalia Tahir Mahmud Gili ya sanar da cewa, an sauke ministan ma’ikatar kula da harkokin adini na kasar Hassan Mu’allim Hussain ne bisa dalilin cewa, an same shi da laifin karbar rashawa a cikin harkokin aikin hajji.

Ya ce ministan ya gayyaci wani kamfani daga wajen domin fasfo ga maniyyatan aikin hajjin bana daga Somalia, amma kuma ya hada bakin da kamfanin wajen karbar wani Karin kudi da suka kai kimanin dalar Amurka 900 a kan kowane maniyyaci guda.

Ya kara da cewa wannan mataki dai yana a matsayin maakin farko ne, bisa la’akari da girman laifin da ministan ya aikata.

3729037

 

 

 

 

 

captcha