IQNA

Wani Malami A Kenya Ya Jaddada Wajabcin hadin kan Musulmi

23:49 - July 08, 2018
Lambar Labari: 3482814
Bangaren kasa da kasa, sheikh Abdulaziz ma'alim Muhammad mai bada fatawa agarin nakuro na kasar Kenya ya yi kira zuwa ga hadin kan musulmi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, sheikh Abdulaziz ma'alim Muhammad malami a garin nakuro na kasar Kenya ya yi kira zuwa ga hada kai tsakanin musulmi baki daya.

Malamin ya ce karfin musulmi na tattare da hadin kansu, kuma rarraba babu abin da za ta kawo musu illa rauni.

Haka nan kuma ya kara da cewa, idan musuli suka mike suka zama masu aiki da koyarwar addininsu, to za su zama abin buga misalia  cikin dukkanin lamurra, da hakan ya hada har da ciyar da tatalin arzikin kasarsu gaba.

3728599

 

 

 

captcha