IQNA

Palastinawa Hudu Sun Yi Shahada A Yau A Ci Gaba Da Gangamin Neman Hakkokinsu

23:51 - April 20, 2018
Lambar Labari: 3482590
Bangaren kasa da kasa, Rahotanni daga Palastinu sun ce akalla Palastinawa 4 aka tabbatar da cewa sun yi shahada a yankin Zirin Gaza sakamakon harbinsu da harsasan bindiga sojojin yahudawan Isra'ila suka yi.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarta cewa, ma'aikatar kiwon lafiya  a yankin zirin gaza ta sheda cewa, a yau Juma'a Sojojin Isra'ila sun bude wutar bindiga  akan palastinawa masu gangami da suke yin kira kan wajabcin dawo musu da hakkokinsu, da kuma bayar da dama ga sauran palastinawa da suka yi hijira da su dawo gida.

Rahotanni sun tababtar da cewa bayan ga shahadar palastinawa hudu a yau, wasu fiye da dari shida sun samu raunuka, kuma ana kula da wasu daga cikinsu a asibitoci daban-daban a zirin Gaza.

Tun daga ranar 30 ga watan maris din da ya gabata ne al'ummar Gaza suka fara gangamin yin kira kan hakkin dawowar palastinawa da Isra'ila ta kora daga yankunansu.

3707267

 

 

 

 

 

captcha