IQNA

An Karrama Mata Da Suka Nuna Kwazo A Harkar Kur’an A Iraki

23:54 - April 19, 2018
Lambar Labari: 3482586
Bangaren kasa da kasa, cibiyar hubbaren Abbas ta girmama mata da suka nuna kwazo a bangaren ayyukan kur’ani mai tsarki a kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Kafil cewa, Sayyid Adnan Musawi daya daga cikin masu kula da lamurran hubbaren Abbas ya bayyana cewa, wannan hubbare ya dauki nauyin karrama mata mambobi na cibiyar kur’ani a wannan hubbare da suka nuna kwazo a tarukan gasar kur’ani mai sarki a kasar Iraki.

Ya ce ko shakka babu babban abin alfahari ne ga dukkanin masu kula da harkokin kur’ani a karkashin cibiyar hubbar Abbas, kan cewa mafi yawan matan da suka fi nuna kwazoa  dukkanin gasar kur’ani da aka gudanar a bangaren harda da kira’a a fadin kasar Iraki, mambobin kwamitin kur’ani ne na wannan cibiya.

Daga karshe ya yi fatan kur’ani mai tsarki ya zama hanyar shiriya da tsira ga dukkanin al’ummar musulmi, kuma ya zama hanyar hadin kansu.

3706643

 

 

 

 

 

 

 

captcha