IQNA

Isra'ila Ta Kaddamar Da Farmaki A Kan Zirin Gaza

23:30 - April 18, 2018
Lambar Labari: 3482582
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar da farmaki da makaman igwa a kan yankin Gaza.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ashraf Qudra kakakin ma'aikatar kiwon lafiya a Gaza ya bayyana cewa, a yau haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar da farmaki da makaman igwa a kan yankin Khuza a da ke Khan Yunus a gabashin Gaza, wanda ya yi sanadiyar jikkatar mutane 5 a yankin.

Bayanin ya ci gaba da sojojin yahudawan sun harba wadannan makaman ne a kan yanun da mutane suke zaune, ba tare da bayyana wani dalili na yin hakan, amma dai babu wanda ya rasa ransa a cewar ma'aikatar kiwon lafiya, sai mutane 5 da suka jikkata.

Baya ga haka kuma wasu motocin sojin Isra'ila masusulke sun yi ta yin sintiri a gefen shingen da ke kusa da iyakan zirin Gaza da kuma yankuna Palastinu da yahudawa suka mamaye.

3706664

 

 

captcha