IQNA

Jam'iyyar Labour Ta Yi Kakkausar Suka Kan Harin Birtaniya A Syria

23:27 - April 18, 2018
Lambar Labari: 3482581
Bangaren kasa da kasa, jam'iyyar labour babbar jam'iyyar adawa ta kasar Birtaniya ta yi kakakusar suka kan yadda Tehresa May ta bi sahun Amurka wajen kai wa Syria.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban jam'iyyar Labour ta kasar Birtaniya Jeremy Corbyn ya bayyana matakin na Theresa May a matsayin raini ga majalisar dokokin  Birtaniya, inda ya ce gwamnati ita kadai ba ta hakkin yanke hukunci kan daukar matakin yaki a wajen kasar Birtaniya ba tare da amincewar majalisar ba.

Corbyn ya ce majalisar dokoki tana gaba da gwamnati, domin al'ummar Birtaniya suka zabi majalisar dokoki, ita kuma majalisa ta kafa gwamnati, a kan hakan majalisa ce kai tsaye take wakiltar al'ummar Birtaniya, yayin da ita kuma take wakiltar majalisa, a kan haka dole ne gwamnatin Theresa May  ta zama mai biyayya ga majalisa, mai karbar umarni daga majalisar Birtaniya, ba daga shugaban Amurka ba.

Yan majalisar dokokin kasar ta Birtaniya da dama dai sun nuna fushinsu matuka dangane da yadda May ta yi gaban kanta wajen kai wa kasar Syria hari tare da Amurka da Faransa, ba tare da iznin majalisa ba, kamar yadda dubban jama'a a birane daban-daban na kasar ta Birtaniya suka yi ta gudanar da zanga-zangar domin nuna kiyayyarsu da wannan mataki da ta dauka da sunan kasarsu alhali al'ummar kasar baa mince da hakan ba.

3706598

 

 

captcha