IQNA

Kamfe Mai Taken Ingila Da Bahrain A Sahu Guda Wurin tak Hakkin Bil Adama

23:40 - January 19, 2018
Lambar Labari: 3482315
Bangaren kasa da kasa, an kaddamar da wani kamfe mai taken Ingila da Bahrain suna a sahu guda wajen take hakkokin bil adama.

Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa ya nakalt daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Lu’u Lu’a cewa, kamfen mai take cut ya fara gudanar da aikinsa ne sakamakon yadda gwamnatin Birtaniya tae hada kai da sarakunan kama karya na larabawa domin danne al’ummominsu.

Wannan yana zuwa ne sakamakon wani shirin da za a gudanar da baje kolin kamfanonin sayar da makaman Birtaniya ne, inda daga cikin wadanda aka gayyata har da wakilan sarakunan kama na kasashen Bahrain, Saudiya da kuma hadaddiyar daular larabawa.

Duk da cewa kasar Birtaniya tana samun mafi yawan cikin makamanta ne daga wadannan kasashe, amma kuma al’ummomin kasar suna ganin bai kamata gwamnatin Birtaniya ta kauda kanta daga irin mulkin kama karya da kisan bayin Alah da wadannan gwamnatoci suke yi da wadannan maamai ba.

Kimanin kashi 76 na mutane masu yawan shekaru a irtaniya suna ganin ya zama wajibi a daina sayarwa sarakaunan wadannan kasashe da makamai, yayin kashi 64 e ganin bai dace a bar su ma da su halarci baje kolin makaman kamfanonin Birtaniya ba.

3683341

 

 

 

captcha