Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na scmp cewa, a cikin kwanakin nan gwamnatin kasar China na yin liken asiri a kan musulmin kasar ta hanyar yin afani da naurorin daukar hoto musamman a garin Sin gyang.
A halin yanzu haka dai dukkanin manyan titunan birnin Sin Gyang cike suk da kamarorin daukar hotunan mutane a ko’ina, domin sanya ido a kan dukkanin harkokinsu da sunan yaki da ta’addanci.
Wannan matakin dai ba shi ne na farko ba, domin kuwa musulmin kasar China wadanda su ne marassa rinjaye a kasar sun jima suna fuskantar matsaloli da takura daga gwamnatin gurguzu ta China.
Haka nan kuma an saka dokoki masu tsauri a yankin tare hana musulmi nuna rashin amincewarsu da ko saba ma dokokin, wanda yin hakan yana tattare da babbar ukuba.
Daga cikin matakan tarukara da gwamnatin China take dauka akan musulmi, har da hana saka sunayen musulunci ga yaran da ake haihuwa, da hana saka hijabi, da kuma hana gudanar da tarukan addin da hana koyar da karatun kur’ani, haka nan kuma ana tilasta ma musulmi kallon tashoshin talabijin na gwamnati.