Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakaltodaga shafin sadal balad cewa, Salen Abbas shugaban bangaren kula da harkokin gasar kurni na jami’ar Azaar ya ce, a cikin watan maris mai zuwa ne za a gudanar da bangaren karshe na kasar Kur’ani mai tsarki ta jami’ar, inda bangarorin harda za su kasance a bangaren hardar kur’ani baki daya, juzui 25, juzui 18.
Ya ci gaba da cewa ya zuwa yanzu an kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da wannan gasa ta hardar kur’ani mai tsarki ta jami’ar azahar da ake yi duk shkara.
Tun a cikin watan da ya gabata ne dai aka fara gasar a matsayin share fage, musamman ganin cewa masu shiga gasar adadinsu yana da yawan gaske.
A yayin gudanar da gasar a matakin karshe babban malmin Azhar da wasu daga cikin malaman jami’an jami’ar gami da wasu jami’an gwamnatin Masar duk za su halartar, kuma za a bayar da kyautuka na musaman ga wadanda suka fi nuna kwazo.
Abin tuni a nan da shi ne, cibiya Azaha ita ce babbar cibiyar ilmimi ta mabiya mazhabobin ahlu sunna a duniya baki daya, wadda aka gina ta tun kimanin shekaru dubu daya da suka gabata.