Sayyid Hassan Ismati shugaban ofishin raya al'adu na Iran a Senegal a zantawarsa da Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa Abul Kasim Fakhri daya daga cikin malaman jami'a a Tehran da ya tarjama kur'ani a cikin harshen Faransanci, wannan kur'ani ya samu karbuwa a tsakanin al'ummar kasar Senegal.
Ya ci gaba da cewa wannan aiki yana daya daga cikin ayyuka na lfahari a kasar Iran tun bayan samun nasarar juyin juya halin muslunci.
Abul Kasim Fakhri ya dauki tsawon shekaru kimanin 20 yana gudanar da tarjamar kur'ani a cikin Faransanci, tare da tabbatar da cewa ya yi tarjamar tasa yadda za ta bayar da ma'anar da ake bukata.
Babbar manufarsa ta wannan aiki dai ita ce samar da hanya mafi sauki ga masu fahimtar harshen Faransanci da su fahimci abin da ke cikin kur'ani mai tsarki da kuma abin da yake koyarwa.