IQNA

Kyautar Kur’ani Bugun Iran Ga Ministan Kasar Senegal

21:49 - January 14, 2018
Lambar Labari: 3482297
Bangaren kasa da kasa, an bayar da kyautar kwafin kur’ani mai tsarki da aka tarjama a cikin harshen Faransanci ga ministan kasar Senegal.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labarai na cibiyar bunkasa al’adun musulunci cewa, jakadan Iran a Senegal Ainullah Qashqawi, da kuma shugaban ofishin raya al’adu na kasar a Senegal Sayyid Hassan Ismati, sun halarci taron bunkasa harkokin al’adun musulunci da aka shirya a a kasar.

A taon sun bayar da kyautar kwafin kur’ani da aka tarjama a cikin harshe faransanci ga Sheikh Konte, minister kuma mai bayar da shawara ga shugaban kasar ta Senegal.

A taron jakadan Iran ya gana da sheikh Konte, kuma sun tattauna muhimman batutuwa da suka alaka a tsakanin kasashen biyu, musamman ta fuskar al’adu da kuma addini, inda dukkanin kasashen biyu sukea  matsayin kasashe masu muhimmanci a kungiya kasashen msuulmi ta duniya.

Haka nan kuma kasar Senegal na daga cikin kasashen Afirka da ske bin tafarkin darikun sufaye, daga ciki ha da sheikh Abdulkadir Jilani, wanda dan Iran da ya kafa wannan darika, kuma yake da dimbin mabiya a kasar ta Senegal da wasu kasashen yammacin Afirka.

Daga karshe an bayar da kyautuka ga jami’an gwamnatin Senegal da suka hada kayan da aka sana’anta da hannu a garin Isfahan na Iran, da kuma wasu littafai na tarihi.

3681801

 

captcha