IQNA

An Nuna Wani Dadadden Kur’ani Mai Rubutun Zinari A Iskandariya

21:21 - January 11, 2018
Lambar Labari: 3482289
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani dadadden kur’ani da aka rubuta shi da ruwan zinari a babban dakin karatu na birnin Iskandariya a kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewa, Muhammad sulaiman shine shugaban cibiyar raya aa’adu ta jahar Iskandariya a kasar Masar, ya bayyana cewa wannan kur’ani yana daga cikin ababen tarihi da ak ajiye da su a wannan dakin karatu tun 2002.

Ya ce daya daga cikin muhimman abubuwan tarihi da suke a wannna wuri a halin yanzu sun hada da wannan kur’ani wanda aka rubuta tuna  cikin karni na takwas kamariya, wato sama da shekaru 600 da suka gabata kenan.

Babban dakin karatu na birnin Iskandariya aya ga littafai na karantaw, akwai ittafai na tarih da sukea  jiye a wurin wadanda ba a taba su sai a duba su.

Kuma kasantuwar wannanbirni ya hada bangarori na mabiya addinai na kiristanci da kuma muslunci, wannan ya saya akwai littafai na dukkanin addinan guda biyu.

Kasar Masar dai na daga ckin kasashen duniya masu dadadden tarihi tun kafin zuwan addinin kiristanci da kuma na muslunci, inda har yanzu kasar tana adana wasu daga cikin kayan tarihi da suke komawa zuwa ga dubban shekaru.

3680962

 

 

captcha