IQNA

A Makokin Rasuwar Sheikh Bamba

An Saka Karatun Kur'ani Da Sautin Karim Mansuri A Senegal

21:18 - January 11, 2018
Lambar Labari: 3482288
Bangaren kasa da kasa, jim kadan bayan sanar da rasuwa babban malamin addini Sheikh Mukhtar Bamba malamin darikar Muridiyya a Senegal an saka karatun kur'ani da sautin Karim Mansuri.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar kula da harkokin al'adun muslunci cewa, a jiya bayan sanar da rasuwa babban malamin addini Sheikh Mukhtar Bamba malamin darikar Muridiyya a Senegal an saka karatun kur'ani da sautin Karim Mansuri a gaban karamin ofishin jakadancin Iran a Dakar.

Sheikh bamba mutum ne da ya yi suna wajen nuna cikakken goyon bayan juyin juya halin muslucni a Iran da kuam marigayi iam Khomeni (RA).

A kwanakin baya wannan malami ya gana da shugaban cibiyar Ahlul bait (AS) Sheikh Hassan Akhtari a birnin Tuba, inda ya bayyana cewa al'ummar Senegal suna cike da kaunar juyin Islama  akasar Iran da kuma marigayi Imam Khomeini (RA).

Tun bayan sanar da rasuwarsa a jiya, an sanar da jyayi a fadin kasar baki dangane da rasuwar tasa.

3681005

 

captcha