IQNA

Sayyid Mustafa Matashin Da Ya Hardace Kur'ani Cikin Watanni Uku

22:27 - October 23, 2017
Lambar Labari: 3482029
Bangaren kasa da kasa, Sharif Sayyid Mustafa matashi ne dan kasar Masar wanda Allah ya yi masa baiwa ta saurin fahimta da hardacewa, wanda ya hardae kur'ani cikin watanni uku.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shafin yad alabarai na Alwatan ya habarta cewa, Sharif Sayyid Mustafa matashi ne dan kasar Masar wanda Allah ya yi masa baiwa ta saurin fahimta da hardacewa, ya koyi tajwidi a cikin 'yan kanaki kafin nan ya fara harda, ya hardae kur'ani cikin watanni uku kacal.

Baya ga haka kuma ya hardace manyan littafan hadisai na ahlu sunna wal jama'a wato Buhari da Muslim a cikin kwanaki 40.

Wannan matashi dan kasar Masar a halin yanzu yana karatun likitanci a jami'a a kasar ta Masar, yayin da kuam a lokaci guda yana mayar da hankali kan lamurra na addini.

A halin yanzu dai Sayyid Mustafa yana da shekaru goma sha takwas ne a duniya, kuma mahaifansa ne masu mayar da hankali ne ga tarbiya da kuma tsarkake ruhi da samun kusanci ga Allah ta hanyar zikirin Allah da ibada.

A wata gasa ta duniya da aka gudanar kan karatun littafi cikin sauri a kasar hadaddiyar daular larabawa ya zo na biyu, ya kuma samu kyautuka da dama.

Wannan matashi a halin yanzu yana daga cikin matasa da ake lissafa su masu baiwa a cikin kasashen musulmi, wanda yake da shirin ci gaba da fadada karatunsa na addini da kuma na likitanci domin amfanin al'ummar msuulmi.

3655826


captcha