IQNA

Azhar Da OIC Sun Yi Allah Wadai Da Kisan Musulmi A Afirka Ta Tsakiya

23:27 - October 22, 2017
Lambar Labari: 3482026
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar muslunci a Masar ta Azhar tare da kungiyar hadin kan kasashen msusulmi sun yi tir da Allah wadai da kisan musulmi da ake a jamhuiya Afirka ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yaum Sabi cewa,a cikin kwanakin baya-bayan na an kasha musulmi fiye da 150 a yankuna daban-daban na Afirka ta tsakiya.

Wasu ‘yan bindiga masu alaka da ‘yan ta’adda na Anti Balaka ne suke kaddamar da wadannan hare-haren a kan musulmi, inda a ko a makon da ya gabata sun ka hari a yankunan kudu kudu maso gabashin kasar, inda suka afka kan masalaci a lokacin sallar zuhur, sun kasha limamin tare da wasu masallata kusan ashirin da biyar.

Azhar ta bayyana cewa dole a dauki dukkanin matakai na kawo karshen wannan kisan kiyashin da ake yi wa musulmi ba gaira ba sabar a kasar ta Afirka ta tsakiya.

Ita ma a nata bangaren kungiyar kasashen musulmi ta bayyana cewa wannan kisan gilla a kan musulmi ba abu ne da za a lamunta da shi ba, kuma dole a dauki matakin dakatar da wannan mummunan aiki.

Yanzu haka dai dubban daruruwan musulmi suka gudu suka bar kasa zuwa kasashe da ke makwabaka da ita, inda suke neman mafaka domin tsira da rayukansu.

Har yanzu dai babu wata daga cikin kasashen larabawa da ta ce uffan kan batun na kisan musulmi a Afirka ta tsaiya, kamar yadda suka gum da bakunansu a kan kisan musulmi  rohingya da ake yi a cikin lokutanan wanda ya dauki hankulan duniya.

3655305


captcha