IQNA

Ayyukan Fadada Cibiyoyin Muslunci A Kasar Morocco

20:43 - October 21, 2017
Lambar Labari: 3482021
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da ayyukan fadada cibiyoyin muslunci a kasar Morocco.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Rabat cewa, gwamnatin kasar Morocco ta fara aiwatar da wani shiri na fadada ayyukan cibiyoyin addinin muslunci a kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa cibiyar bayar da horo kan harkokin muslunci ta kasada kasa da ke Moroco ita ce kan gaba wajen aiwatarda wannan shiri, wanda zai ci gaba da bunkasa.

Sarki Muhammad na shida na Morocco shi e ya jagoranci kaddamar da shirin wanda zai mayar da hankali wajen ilmantarwa da kuma wayar da kai yin ilimi dadai da koyarwar addini, maimakon bin wasu masu yada akidun ta’addanci a cikin addinin musulunci.

Akwai masu yin nazari a wannan cibiya daga kasashen duniya daban-daban, da suka hada da kasashen Mali, Iory Coast, Guinea, Tunisia, Faransa, Nigeria da kuma Chad.

An gina cibiyar wadda take da fadin mita dubu 10, da kujeru 640, sai kuma gadajen kwana 350, kudin aikin gina cibiyar ya kama dala miliyan 17.5 baki daya.

Ahmad Taufiq minister mai kula da harkokin addini a kasar Morocco ya bayyana cewa, yanzu haka wannan cibiya ta iya yaye dalibai da suka kai 778 daga kasashen duniya, wadanda za su rika aikin wayar da kan jama’a bisa hakikanin koyarwar addinin mulsunci, ba tare da haifa da rikici ko kafirta musulmi ba, ko kuma tunzura mutane da fatawoyi na ta’addanci.

3654979


captcha