IQNA

Taron Bincike Kan Tarihin Muslunci A AfirkaTa Kudu

23:13 - March 05, 2016
Lambar Labari: 3480203
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman taro a kasar Afirka ta kudu domin bahasi kan matsayin muslunci da tarihinsa a wannan kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anadolu Agency cewa, Zain Alkaji wanda ya shiya gudanar da wannan zaman taro ya bayyana cewa, ba a rubuta tarihi daidai ba kan muslunci a kasar Afirka ta kudu.

Ya ci gaba da cewa tun shekaru masu yawa da suka gabata ne addinin muslunci ya shigo Afirka ta kudu, duk kuwa da cewa akasarin kabilun kasar suna kan addinansu da al’adunsu an gargajiya ne, amma dai duk da haka akwai muslunci a kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa bayan da muslunci ya shigo cikin nahiyar Afirka, bai tsaya wani bangare na nahiyar ba kawai, ya ci gaba da bazuwa zuwa sassa, duk kuwa da cewa bazawars a awasu yankuna ta kasance a hankali.

Ya ce a halin yanzu addinin muslunci shi ne addinin da ya fi saurin karbuwa atsakanin al’ummar kasar Afirka ta kudu, da hakan ya hada dukaknin yankunan kasar baki daya.

Daga ciki kuwa har da yankuna na mazauansu kabilun kasar ne masu bin addinin gargajiya tun kaka da kakani, inda wasunsu sukan bayyana akidarsu ta muslunci wasu kuma sukan boye saboda wasu dalilai.

Malamin ya ce babban abin da ke a gaban musulmin kasar a halin yanzu shi ne yada wannan addini tare da bayyana ma mutane manufrsa ta hakika da kuma koyarwqarsa, maimakon yadda mutane suka dauki muslunci da koyarsa.

Abin takaici shi ne yadda wasu daga cikin al’ummomi suke daukar cewa musulunci addinin ta’addanci ne, alhali kuwa shi ne addini da ke kira zuwa ga girmama dan adam da tausayi da jin kai.

3480605

captcha